Zaɓen Gwamnoni: Jami’an Tsaro Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa
Ya yin da ya rage kasa da mako daya a gudanar da zaben gwamnoni da na yan’majalisar dokokin jihohi a kasar nan, Jami’an tsaro sun ce, sun gano wasu shirye-shiryen da manyan jam’iyyu masu adawa da juna ke yi domin tayar da fitina a lokacin zaben a wasu Jihohi.