Zaɓe: ƙungiyar kiristocin ƙasar nan ta buƙaci mabiyanta da su karɓi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa
Kungiyar kiristocin ta Ƙasa, CAN, reshen Arewacin kasar nan ta bukaci duk mabiyanta da su kwantar da hankalinsu biyo bayan ayyana Bola Ahamad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar nan da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta yi.