• Home  
  • CP Ibrahim Bakori Yasha Alwashin Yaki Da Yan Daba Da Masu Kwacen Waya A Kano
- Babban Labari

CP Ibrahim Bakori Yasha Alwashin Yaki Da Yan Daba Da Masu Kwacen Waya A Kano

  Sabon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatarwa da al’umma jihar cewa zai yi yaki da masu aikata laifukan fadan daba wanda yake da alaka da kwacen waya da kuma shan miyagun kwayoyi . Kwamishinan yan sandan ya bayyana hakan ne a ganawarsa ta farko da manema labarai, a wajen […]

 

Sabon kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatarwa da al’umma jihar cewa zai yi yaki da masu aikata laifukan fadan daba wanda yake da alaka da kwacen waya da kuma shan miyagun kwayoyi .

Kwamishinan yan sandan ya bayyana hakan ne a ganawarsa ta farko da manema labarai, a wajen shakatarwar manyan jami’an sanda dake unguwar Bompai Kano.

Bakori,  ya ce zai hada kai da sauran hukumomin tsaro don ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, inda ya bukaci hadin kan al’umma domin cimma nasarar da ake da bukata.

Kwamishinan yan sandan, ya kara da cewa tuni ya tattauna da manyan jami’an yan sandan jihar , don magance matsalar fadan daba, tare da gabatar da kudirin kara horas da yan sandan dabarun gudanar da aiki.

Haka zalika ya ce zai gana da baturen yan sanda musamman wadanda suke kan iyaka da jahohin da suke fama da matsalar tsaro da garkuwa da mutane.

Ya kuma ce zai amfani da fasahar sadarwa wajan gudanar da aikin sa, tare kuma da wayar da akan al’umna kasancenwar aikin tsaro na kowa ne ba iya yan sanda ba.

Dangane da shirye-shirye bukukuwan sallah dake karatowa kuma, Cp Bakori ya ce al’ummar jaihar Kano, za su yi bikin sallarsu cikin kwanciyar hankali da lumana domin sun yi dukkanin shirin da yakama don tabbatar da tsaro.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai