A cigaba da kawo muku labari game da gobarar da ta tashi a kotun ƙolin Najeriya da ke Abuja a yau.
Shugaban Hukumar agajin gaggawa a Babban Birnin Tarayya, Abbas Idris, ne ya tabbatar wa da majiyarmu da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami’an kai ɗauki suka isa harabar kotun.
Sai dai ya tabbatar da cewa wutar ta shafi wani ɓangare ne kawai na kotun.
A cewarsa: ofisoshi biyu ne lamarin ya shafa kuma babu wanda ya rasa ransa a yayin gobarar.
Ya ƙara da cewa yanzu haka jami’an kai ɗauki sun samu nasarar shawo kan wutar.
Bayanan farko-farko da ke fitowa dai sun nuna cewa wutar lantarki ne ya haddasa gobarar.