• Home  
  • Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari
- Babban Labari - Siyasa

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari

Ɗan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya bayyana cewa, ya amsa kiran al’ummar mazaɓarsa ne na tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai. Ya ce, burinsa shi ne ya ɗora kan kishin ƙasa da jajircewar mahaifinsa wajen gina mazaɓarsa, jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya. Yayin da yake jawabi a Daura bayan wani […]

Ɗan tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya bayyana cewa, ya amsa kiran al’ummar mazaɓarsa ne na tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai.

Ya ce, burinsa shi ne ya ɗora kan kishin ƙasa da jajircewar mahaifinsa wajen gina mazaɓarsa, jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Yayin da yake jawabi a Daura bayan wani taron masu ruwa da tsaki da mambobin jam’iyyar APC, Yusuf ya bayyana cewa ya girma yana kallon yadda mahaifinsa yake bayar da gudunmawa wajen ci gaban Najeriya, tun daga lokacin aikin soja har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Ya bayyana cewa, bayan amincewa da kiran, ya dawo gida ne domin neman sahalewar mazaɓarsa don ya wakilci mazaɓar Daura, Mai’adua da Sandamu.

Ya ƙara da cewa, babban abin da zai fi mayar da hankali a kai idan aka zaɓe shi ne ci gaban matasa.

“Matasa ne ƙashin bayan kowane ci gaba mai ma’ana. Zan mayar da hankali kan ci gabansu domin magance matsaloli da dama,” in ji shi.

A cewarsa, kodayake ya taɓa cewa ba zai shiga siyasa ba, yanzu ya canza shawara kamar yadda ƙaddara take.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da zama a cikin mazaɓarsa don ya fahimci buƙatunsu sosai yadda zai sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata.

Ya kuma ƙara bayyana cewa, kodayake yana iya zama abu mai wuya ya kai matsayin farin jini da ƙauna da mahaifinsa yake da shi, zai yi iyakacin ƙoƙarinsa wajen ganin ya cika burin jama’a kuma ya yi wa mutanensa hidima cikin gaskiya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai