Tsofaffin ‘yanwasan Super Eagles Ahmad Musa da Shehu Abdullahi sun amince da fafatawa Kano Pillars wasa a kakar wasa ta bana ta 2024 zuwa 2025.
Idan za a iya tunawa Ahmad Musa tsohon danwasan Kano Pillars ne inda ya taka leda a kungiyar daga 2009 zuwa 2010 ya fafata wasanni 25 ya jefa kwallaye 18 sannam ya tsallaka zuwa nahiyar Turai.Shima Shehu Abdullah ya zauna a Kano Pillars a 2012 zuwa 2014 amma bai fafatamata wasa ba.
Wadannan ‘yan wasa sun shahara musamman wajen baiwa Super Eagles gudun mawa da kuma jerin kungiyoyin kwallon kafan da suka fafatawa wasanni a nahiyar Turai.
Haka zalika Ahmad Musa ya taba sake fafatawa Kano Pillars wasa a ‘yan shekarunnan a shakarar 2021 inda ya fafata wasanni 8 amma bai samu damar jefa kwallo ba, kai tsaye za ace wannan ne karo na uku da zai fafatawa Pillars wasa.
Sai dai kuma dawowar wadannan ‘yan wasa ba karamar martaba zai janyowa Kano Pilars ba dama ita kanta gasar ta NPFL baki daya, domin kuwa za a dinga tururuwar kallon wasannin Pillars dama yawan haska wasanninsu a talabijin.
Amma irin wannan abu da ‘yan wasan su kayi ya samo asali a duniyar kwallon kafa, domin mafiya yawan ‘yan wasan kwallon kafa a duniya sukan koma asalin kungiyoyin kwallon kafan da suka fara fitowa domin karasa wasanninsu na tsufa a can, to Ahmad Musa da Shehu Abdullahi suma hakan ta faru dasu.
Yanzu dai ta tabbata ‘yan wasan guda biyu za su fafatawa Pillars wasannin kakar wasa guda daya kana su rataye takalmansu ko kuma su sake komawa wasu kungiyoyin kwallon kafan domin ci gaba da taka leda.