Wasu ‘yan ta’adda masu satar mutane sun kai mummunan hari garin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko-Wassagu ta Jihar Kebbi a Arewa Maso Yammacin Najeriya, inda rahotanni suka tabbatar da cewa sun yi awon gaba da uban ƙasa na yankin da kuma aƙalla wasu mutane tara.
An ce ‘yan ta’addar sun kashe mutun ɗaya da kuma sun raunata wasu mutane uku da a halin da ake ciki su na asibiti a kwance.
‘Yan ta’addar sun kai wannan hari ne a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi da ta gabata.
- Dawowar Ahmad Musa da Shehu Abdullahi Zuwa Kungiyar Kano Pillars.
- Tsoffin ‘Yan Sanda 500 Sun Mutu Suna Neman Haƙƙinsu
Wani mazaunin ne ya bayyana, wa kafar yaɗa labarai ta BBC a bisa amanar cewa ba za a bayyana sunansa ba.
Ya ce : ”Da misalin ƙarfe ɗaya na daren Asabar ɗin da ta gabata ne ɓarayi suka shigo garin Kanya, inda suka kama mutane 10, ciki har da uban ƙasar Kanya, Alhaji isa ɗaya wanda aka kama tare da iyalansa.
Majiyar ta ce ‘yan ta’addar sun tafi da mutum 10, kuma sun kashe mutum ɗaya, sa’annan sun jikkata mutum biyu mace da namiji wanda yanzu haka suna kwance a asibiti suna karɓar magani.”
Mutumin ya bayyana cewa mutanen yankin na zaune cikin halin fargaba da tashin hankali sakamakon jimamin da suke yi na faruwar wannan al’amari.
Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu ba a samu yin magana da waɗanda suka sace mutanen ba, balle ma a fara tunanin yadda za a yi a dawo da su ga iyalansu.
”Ba su tambayi komai ba sun dai shiga gidajen mutane suka tafi da waɗanda suka kama, kuma har yanzu ba a ji daga garesu ba.’’
ASP Nafi’u Abubakar, babban jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Kebbi, ya tabbaar da faruwan lamarin.
Inda ya ce a lokacin da rundunar ta sami labarin, jami’anta sun garzaya yankin amma ba su cimma ɓarayin ba.
Ya ce: ”Ɓarayin sun ƙetaro ne daga jihar Zamfara, kuma mun sami rahoton cewa sun tafi da mutum tara bayan sun kashe mutum guda a lokacin harin.”
Babban jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Kebbi ya ƙara da cewa wannan harin dai ya zo ne a lokacin da aka kwashe tsawon watanni ba a sami aukuwar irin haka ba a yankin amma a halin yanzu rundunar ta baza jami’anta a sassa daban-daban na yankin domin tabbatar da zaman lafiya.