Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC), ta amince da bai wa duk mutumin da aka killace tallafin Naira 100,000 domin daƙile yaɗuwar cutar Ebola a Abuja.
Darakta-Janar na hukumar, Dakta Jide Idris ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce kuɗin za su taimaka wajen biyan kuɗin abinci, masauki da sauran buƙatun iyalan mutanen da aka killace saboda sun yi hulɗa da wanda aka tabbatar yana ɗauke da cutar.
Ya ce wasu daga cikin mutanen sun koka kan wahalar biyan kuɗin buƙatunsu na yau da kullum yayin da suke bin ƙa’idojin kariya da hukumomin lafiya suka gindaya.
“Mun biya kuɗin masaukinsu da abincinsu. Wasu kuma sun nemi tallafin kuɗi domin su kula da iyalansu,” in ji Idris.
Ya ƙara da cewa ba a shirya bayar da wannan tallafi tun farko ba, amma an ga buƙatarsa saboda yanayin gaggawar da ake ciki.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da duba lamarin bisa yadda yanayin cutar zai kasance.
Idris ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su tanadi kuɗi da kayan aikin da ake buƙata domin tunkarar irin waɗannan matsalolin lafiya.
Ya bayyana cewa bai kamata nauyin tallafa wa waɗanda abin ya shafa ya rataya a wuyan Gwamnatin Tarayya kaɗai ba.
An amince da tallafin ne yayin da hukumomin lafiya ke ƙoƙarin hana yaɗuwar Ebola bayan tabbatar da samun mutum ɗaya da ta shigo da cutar Abuja a ranar 20 ga watan Oktoba.
Idris ya ce an gano mutane 53 da suka yi hulɗa kai-tsaye da mai cutar, waɗanda ake sa ido kan yanayin lafiyarsu.
Mutanen sun haɗa da ma’aikatan lafiya, ’yan gidan marar lafiyar, ma’aikatan gida da kuma waɗanda suka taimaka wajen ɗaukar samfurin gwajin cutar.
NCDC na ci gaba da sa ido kan waɗannan mutane a tsawon kwanaki 21, domin tabbatar da komai lafiya.
Duk wanda aka gani da alamomin cutar za a duba lafiyarsa tare da yi masa gwaje-gwajen da suka dace.
Manufar wannan ita ce gano duk wata alamar cutar da wuri da kuma hana ci gaba da yaɗuwarta.
