EFCC Ta Gayyaci Tsohon Ministan Sharia Abubakar Malami

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gayyaci tsohon ministan shari’a a Najeriya Abubakar Malami, SAN, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya ce hukumar ta gayyace shi domin ya yi bayani a kan wasu abubuwa da bai bayyana ba, kuma ya bayar da tabbacin girmama gayyatar.

” A matsayina na ɗan ƙasa mai bin doka da oda kuma mai kishin ƙasa, na kuduri aniyar girmama wannan gayyata.

Na yi imani da muhimmancin gaskiya, riƙon amana da kuma rike gaskiya a harkokin mulki — waɗannan ƙa’idoji ne da na dade ina goyon baya tare da tsayawa a kai, a iya shekaru danayi a aikina na hidimar jama’a” kamar yadda ya wallafa a shafinsa.

Ya kuma shaida wa ƴan ƙasar zai ci gaba da sanar da su abin da zai biyo baya, a cewar sa ‘domin kowa ya kasance da masaniyar me zai je ya koma saboda halin rayuwa na yau da gobe da kuma tarihi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *