Rundunar yan sandan jihar Neja, ta kama wani Fasto mai suna, Vincent Emmanuel, cikin gungun mutanen da ake zargi da kwarewa wajen satar yara da yin safararsu tare da siyarwa, a sassan dabam-daban na duniya.Kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.Ya ce, asirin mutanen ya tonu ne bayan kama wata mata mai suna ,Victoria Chukwumezie, akan Titin Dikko Junction dauke da yara uku da ake zargin na sata ne.Wasiu Abiodun, ya kara da cewa jami’an sun bibiyi batan wata yarinya mai shekaru biyu wadda aka ceto a jihar Delta bayan an sace a Neja sannan aka siyar da ita ga, Fasto Vincent Emmanuel , a Abuja.
- EFCC Ta Gayyaci Tsohon Ministan Sharia Abubakar Malami
- Hamɓararren shugaban Guinea Bissau ya isa Senegal
Vincent Emmanuel, ya sayi karamar yarinyar kan kudi naira miliyan biyu da dubu dari takwas, inda shi kuma ya siyar da ita ga wata mata dake zaune a kasar Burtaniya kan kudi sama da naira miliyan uku.Rundunar ta yanzu haka tana tsare da mutane 8 kuma zata gurfanar da su, a gaban kotu da Zarar ta kammala bincike.
