• Home  
  • Fitaccen Dan Wasan Tseren Motoci Jenson Button Zai Yi Ritaya
- Babban Labari - Labarai

Fitaccen Dan Wasan Tseren Motoci Jenson Button Zai Yi Ritaya

Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka […]

Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci.

Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota.

Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000