Gobara ta ƙone ajujuwa da ɗakunan ajiya da kuma babban ɗakin taro a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSS) da ke Jalingo, a Jihar Taraba.
Gobarar ta lalata kusan dukkan ajujuwan makarantar da littattafan karatu, da babban ɗakin jarabawa, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin karatu a makarantar.
Ana zargin gobarar ta fara ne daga wani aji, sannan ta bazu cikin sauri zuwa sauran ajujuwa da gine-ginen makarantar. Koƙarin ɗalibai da ma’aikata wajen shawo kanta ya hana ta cinye dukkan ajujuwan makarantar gaba ɗaya.
Ba a samu asarar rai ba, yayin da gwamnatin jihar ta bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbabin lamarin.
Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wata gobara makamanciya da ta lalata Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Wukari da kuma shaguna da dama a Jalingo.
Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Taraba, Dakta Augustina, ta kai ziyara wurin tare da rakiyar Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Idris Goje, da Sakataren Ma’aikatar, Mista Benjamin Zantimaba, sun duba gine-ginen da gobarar ta lalata.
Dakta Augustina ta yaba wa mahukuntan makarantar, musamman Shugaban Makarantar, Malam Ibrahim Modibbo, bisa ƙoƙarin da suka yi wanda ya hana gobarar yaɗuwa fiye da haka.
Ta tabbatar wa makarantar cewa gwamnati za ta gudanar da cikakken tantancewar asarar da aka yi domin bayar da tallafin da ya dace tare da dawo da gine-ginen da abin ya shafa cikin gaggawa.
- Ƴan sanda sun kama dillalin miyagun kwayoyi da wasu Mutane 5 a Kano
- Magoya bayan Kwankwaso sun ƙi halartar taron Gwamna Abba
Ta jaddada muhimmancin ƙarfafa matakan tsaro a makarantu, ciki har da duba masu shigowa ba bisa ka’ida ba akai-akai da inganta hanyoyin kariya daga gobara, domin kauce wa faruwar irin wannan a gaba.
A nasa ɓangaren, Shugaban Makarantar, Ibrahim Modibbo, ya nuna godiya ga ziyarar gaggawar da Dakta Augustina ta kai da kuma kulawar da ma’aikatar ta nuna, yana mai cewa wannan zai ƙara ɗaga ƙwarin gwiwar ma’aikata da ɗaliban da lamarin ya shafa.
A ƙarshe, an jaddada buƙatar gwamnatin Jihar Taraba ta samar da motocin kashe gobara masu aiki yadda ya kamata domin tunkarar irin waɗannan lamurra a nan gaba.

