A daidai lokacin da raɗe-raɗen sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC ke ci gaba da ɗaukar hankali a Kano, an sake ganin wata sabuwar ɓarakar da ke nuna akwai tsamin dangantaka tsakanin gwamnan da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A ƙarshen mako, wasu manyan magoya bayan Kwankwaso sun ƙaurace wa taron yaye ɗaliban da suka koyi sana’o’in hannu, wanda gwamna Abba ya jagoranta a fadar gwamnatin jihar.
Rashin ganin fuskokin wasu fitattun ‘yan Kwankwasiyya a taron ya ƙara dasa alamar tambaya kan alaƙar da ke tsakaninsu.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka ga gwamnan a bainar jama’a bayan shafe fiye da mako guda ba tare da fitowa fili ba.
Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai Hashim Sulaiman Dungurawa, wanda makusancin Kwankwaso ne. Sai dai a wurin taron, Abdullahi Zubairu Abiya ne ya halarta a matsayin sabon shugaban jam’iyyar NNPP a jihar.
Akwai kuma wasu waɗanda ake gani makusantan Kwankwaso ne da suke tare da Kwankwaso da ba su halarci taron ba.
Daga cikinsu akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso; Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr Yusuf Kofar Mata; da Kwamishinan Tsaro na Kano, AVM Ibrahim Umar mai ritaya, tare da Shugaban Ma’aikata, Abdullahi Musa.

