• Home  
  • Gobara ta sake tashi a wata kasuwa a Kano
- Babban Labari - Labarai

Gobara ta sake tashi a wata kasuwa a Kano

Wata gobara da ta tashi da asuba ta lalata akalla shaguna 50 a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose Market da ke unguwar Dakata a Jihar Kano. Shugaban kwamitin kashe gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara ne misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Juma’a. Ya bayyana cewa […]

Wata gobara da ta tashi da asuba ta lalata akalla shaguna 50 a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose Market da ke unguwar Dakata a Jihar Kano.

Shugaban kwamitin kashe gobarar kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce gobarar ta fara ne misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa mafi yawan shagunan da gobarar ta shafa na kanana ne da ke harkar sarrafa mai da kuma sake yin amfani da robobi da ledoji.

A cewarsa, har zuwa ƙarfe 5:40 na safiyar Juma’a gobarar na ci gaba da ƙone shagunan. “Daga abin da muka gani a farko, shaguna kusan 50 sun kone, kuma gobarar na ci gaba da ci. Har yanzu muna jiran jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano,” in ji shi.

Chula ya ƙara da cewa sun yi ƙoƙarin sanar da hukumomin da abin ya shafa, kuma sun tabbatar da cewa sun samu labarin.

“Mun yi iya ƙoƙarinmu wajen kiran su da sanar da su halin da ake ciki. Yanzu haka ma ina jin karar motarsu,” ya ƙara da cewa.

Har yanzu ba a tantance girman asarar da yiwuwar rasa rayuka ba, sai dai ’yan kasuwa sun nuna damuwa kan jinkirin da hukumomin agaji suka yi wajen kai dauki.

Wannan gobarar ta zo ne kasa da mako guda bayan makamanciyarta da aka samu a Kasuwar Singer, inda aka ce fiye da ’yan kasuwa 1,000 suka yi asarar da ta kai biliyoyin naira.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai