Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar ƙirƙirar sabbin masarautu 13 wadda za ta ba da damar naɗin hakimai sama 111 a faɗin jihar.
Sabbin masarautun da gwamnan ya ƙirƙira sun haɗa da: Burra, Duguri, Dambam, Bununu, Lere, Darazo, Jama’a, Lame, Toro, Ari, Warji, Giade da kuma masarautar Gamawa.
Da yake jawabi a gidan gwamnati, Bala Mohammed ya gargadi masu son siyasantar da lamarin ko kawo cikas wajen aiwatar da dokokin, yana mai cewa hukumomin tsaro za su dauki matakin da ya dace.
Ba za mu lamunci duk wanda zai yi ƙoƙarin tayar da hankali ko ya kawo rikici ba. Duk wanda aka kama yana ƙoƙarin ɓata tsarin nan, doka za ta yi aikinta,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa duk wani jami’in gwamnati ko shugaba na gargajiya da ya aikata abin da zai ƙalubalanci manufar dokar, za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.
A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Y. Suleiman, ya bayyana cewa dokar ta samo asali ne daga tattaunawa mai faɗi da aka yi da masu ruwa da tsaki, ciki har da sarakuna, ƙungiyoyin farar hula, da masana.
Ya ce dokar ta tabbatar da muradin gwamnati wajen kusantar da mulki da ci gaba ga jama’a, tare da ƙarfafa harkokin masarautu da inganta ayyukan gwamnati a yankunan da ke buƙatar kulawa.
“Wannan doka ba iya faɗaɗa tsarin mulki za ta yi ba, domin kuwa za ta tabbatar da adalci da daidaito ga kowane yanki na Jihar Bauchi,” in ji Kakakin Majalisar.
Ya kuma sanya hannu kan dokar tsarin fansho ta ma’aikatan kananan hukumomi, tare da alƙawarin biyan bashin fansho da ladabtarwa da ake bin tsoffin ma’aikata.
Kazalika, gwamnan ya amince da Dokar Ƙarin Kasafin Kuɗi ta 2025, domin tabbatar da ci gaban ayyukan da ake aiwatarwa a jihar.

