Tag: Bauchi

Babban Labari

Gwamnan Bauchi Na Shirin Sauya Sheka Zuwa ADC

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana shirinsa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar ADC, inda ya ce jam’iyyar na da damar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027. Idan Bala Mohammed ya sauya shekar, ADC ta samu gwamna mai ci na farko, wanda hakan zai kara mata karfi a kan tsofaffin gwamnoni da tsofaffin […]

Babban Labari Labarai

Gwamna Bala Abdulkadir Ya Musanta Zargin Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa PRP

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ƙaryata zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga PDP zuwa jami’yyar PRP. Jita-jitar ta samo asali ne bayan Sakataren jam’iyyar PRP na Bauchi, Hon. Wada Abdullahi, ya ce ba za su karɓi gwamnan zuwa jami’yyarsu ba. Ya ce gwamnan bai cika ƙa’idojin da PRP ke buƙata ba a shugabancinsa […]

Babban Labari Labarai

Yau Za A Yi Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi

A yau Juma’a ne za a gudanar da jana’izar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ya rasu, ranar Alhamis, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Sheikh Dahiru wanda jagora ne na darikar Tijjaniyya ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma yana da shekara 100 da ƴan watanni. Shehin malamin ya rasu […]

Babban Labari Labarai

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu

Jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne da asubahin ranar Alhamis. Malamin ya rasu ne a wani asibiti da ke jihar Bauchi.sakamakon ƴar gajeriyar jinya. Majiyoyi daga iyalansa sun ce za a yi jana’izar shehin malamin ne a ranar Juma’ah. Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya rayu tsawon shekaru 100 a […]

Babban Labari Labarai

Mutane 7 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Jigawa

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse. Ya ce hatsarin ya […]

Babban Labari Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Dan Uwansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan, a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a. […]

Babban Labari Labarai

Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane 58 A Bauchi

Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi. Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar. Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu kwamitoci biyu kan yaki […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai