• Home  
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas

Majalisar zartaswar jihar Jigawa ta amince da fitar da naira biliyan 2.5 don nazarin yanayin kasa domin gano yuwuwar samun makamashin Uranium da ɗanyen mai da iskar gas a cikin jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa da Wasanni da Al’adu na Jihar, Hon. Sagir Musa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema […]

Gwmnan Jihar Jigawa, Umar Namadi Dan Modi

Majalisar zartaswar jihar Jigawa ta amince da fitar da naira biliyan 2.5 don nazarin yanayin kasa domin gano yuwuwar samun makamashin Uranium da ɗanyen mai da iskar gas a cikin jihar.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa da Wasanni da Al’adu na Jihar, Hon. Sagir Musa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron majalisar zartarwar jihar a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa, amincewa da binciken a wasu keɓantattun wurare, ya biyo bayan karatun share fage na shekaru da rahotanni kan albarkatun ma’adanai daban-daban a fadin jihar Jigawa.

Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki.

A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na binciko albarkatun ma’adanai na jihar don haɓaka tattalin arzikin cikin gida mai ɗorewa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai