A yau ake sa ran wakilan gwamnatin tarayya za su yi wani zama na musamman da shuwagabannin ƙungiyar ƙwadago da misalin ƙarfe 2 na rana.
Wannan zama dai za a yi shi ne game da cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta tabbatar bayan ayyana hakan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi.
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa Joe Ajaero a yayin hirarsa da gidan talabijin na Channels.
Sannan ya tabbatar da cewa a daren jiya ne, jami’an sabon gwamnatin suka tuntuɓe shi domin tabbatar da wannna zama.
Ya ce matsayar ƙungiyar shi ne, idan har shugaba Tinubu na da niyya mai kyau game da cire tallafin man fetur, to wajibi ne ya samar da wata hanya da za a waraware matsalar da hakan ka iya jawowa.
Cikin abubuwan da shugaban ƙwadagon ke sa ran gwamnatin za ta samar akwai farfaɗo da matatun mai guda huɗu na ƙasar nan da samar da hanyar zirga-zirga ta yau da kullum ga ma’aikata.