Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamiti na musamman da zai samar da motoci masu amfani da Iskar Gas da kuma tashoshi na sayar da isakar gas domin karfafa shirin fara amfani da motoci masu amfani da shi a fadin kasar nan.
Kwamitin zai fara aiki ne a Jiihar Legas a karkashin jagorancin kwamitin shugaban kasa a kan amfani da Iskar Gas.
Shugaban kwamitin na kasa, Micheal Oluwagbemi, ya ce an ƙaddamar da tashoshin Iskar Gas ne a fadin Nijeriya don ya zama wani mataki mai muhimmanci a hankoron da gwamnati take yi na tabbatar da an fara kaurace wa amfani da man fetur a motoci.
Ya kuma kara da cewa, cibiyar samar da Iskar Gas ɗin da aka kaddamar za ta taimaka wajen samar da makashin da ba ya cutar da yanayi za kuma ta jagoranci makomar tattalin arzikin ƙasa a nan gaba, an dai kaddamar da tashar ne a KM 42, a Lekki-Epe ta jihar Legas.
Idan za a iya tunawa an sanar da kafa tashoshin samar da Iskar Gas 7 a sassan Nijeriya.
Kwamitin ya kuma mika motoci da aka sauya su suka fa