An Ɓullo Da Sabuwar Manhajar Karatu A Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabuwar manhajar karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatun da za a fara a watan Satumbar bana a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne da nufin rage nauyin karatu kan ɗaliban da kuma inganta tsarin koyarwa a faɗin ƙasar.

Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ce ta bayyana hakan a madadin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa a ƙarshen makon jiya.

Ministar ta ce an gudanar da bitar ce tare da haɗin gwiwar Hukumar Bincike da Cigaban Ilimi ta Nijeriya (NERDC), da Hukumar Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko Universal Basic Education Council UBEC, da NSSEC, da NBTE, da sauran masu ruwa da tsaki.

“Sabon tsarin zai kawo daidaito a darussan da ake koyarwa wajen zurfafawa da kuma koyar da ilimi a aikace.

“A matakin farko, ɗaliban Firamare na aji 1-3 za su ɗauki darussa 9-10, yayin da waɗanda ke Firamare aji 4-6 za su ɗauki darussa 10-12.

“A Ƙaramar Makarantar Sakandare yawan darussan za su kai 12-14 ne; ɗaliban babbar sakandare za su ɗauki darussa 8-9; sai kuma makarantun fasaha za su ɗauki darussan 9-11,” in ji ta.

Farfesa Ahmad ta jaddada cewa, manhajojin da aka yi wa kwaskwarima an tsara su ne domin rage yawan abubuwan da ke ciki, da ba da ƙarin lokaci don koyo, da kuma tabbatar da cewa ilimi ya ci gaba da dacewa da abubuwan da suke faruwa a duniya a yau.

Ma’aikatar ta yaba wa masu ruwa da tsaki bisa jajircewar da suka yi tare da ba su tabbacin cewa za a aiwatar da sabbin manhajoji tare da sanya ido sosai don tabbatar da samun karbuwa mai inganci da samun sauyi cikin sauƙi a makarantu a fadin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *