Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ceto ɗalibai da malamai da aka sace a jihohin Oyo da Borno.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a madadin shugaban ƙasar yayin wani taro na musamman kan tsaro da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Idris ya bayyana garkuwa da ɗaliban da malamansu a matsayin wani mummunan lamari ga makomar Najeriya, tsarin ilimi da kuma ƙimar al’ummar ƙasar.
Ya ce Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin amfani da dukkan hanyoyin da doka ta tanada domin tabbatar da kuɓutar da waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Aminiya ta ruwaito cewa an yi garkuwa da wasu ɗalibai da malamai a Jihar Oyo, yayin da kuma wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai hari wata makaranta a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba da ke Jihar Borno, inda a nan ma aka ce yara aƙalla 42 sun ɓace.
Ministan ya ce hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da rundunar soji, Hukumar DSS, ’yan sanda, Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), na haɗa kai wajen gudanar da aikin ceto.
A cewarsa, ana ci gaba da tattara bayanan sirri, sanya ido ta sama, haɗin gwiwa da al’umma da kuma ayyukan bincike da ceto ba tare da tangarɗa ba.
Idris ya ce gwamnatin Tinubu na ɗaukar matakan yaƙi da rashin tsaro ta hanyar haɗa ƙarfin soji, amfani da bayanan sirri, fasahar zamani da kuma sake fasalin tsarin tsaro.
“Abin da ya bambanta martanin gwamnatin Tinubu shi ne ba amfani da ƙarfi kaɗai ba, har ma da bin hanyar bayanan sirri da kuma aiwatar da gyare-gyaren da aka daɗe ana buƙata a fannin tsaro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa daga cikin muhimman sauye-sauyen da ake son aiwatarwa akwai samar da tsarin ’yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro a matakin ƙananan hukumomi da al’umma.
Ministan ya kuma ce Shugaba Tinubu na ci gaba da tuntuɓar Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da hukumomin tsaro domin tabbatar da kuɓutar da waɗanda aka sace.
“Ga iyalan da har yanzu ’ya’yansu ke hannun masu garkuwa da mutane, muna jin raɗaɗin da kuke fuskanta.
“Gwamnati za ta ci gaba da amfani da dukkan ikon da take da shi har sai an dawo da su gida lafiya,” in ji Idris.
