Gwamnatin Najeriya ta damƙawa ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da kuma ƙungiyar ɗalibai ta NANS motocin bas masu amfani da iskar gas guda 64 a jiya Lahadi, 29 ga Satumbar 2024.
Bikin bada motocin ya gudana ne a fadar gwamantin tarayya da ke Abuja, duka cikin bikin cika shekara 64 da samunƴancin ƙasar.
- Kashi 40 Na Ƴan Najeriya Na Samun wutar Lantarki Na Awa 20 A kullum – Gwamnati
- Akwai Alaka Tsakanin Girman Yara Da Abincin Da Su Ke Ci: UNICEF
Yayin da ya ke jawabi a gurin taron, Ministan Kuɗi Wale Edun ya ce wannan ɗaya ne daga cikin yunƙurin gwamnatin na sauƙaƙa farashinzirga zirga wanda ya hauhawa tun bayan cire tallafin man fetur.
Ministan ya ƙara da cewa hikimar ba da motocin a jajiberen bikin ƴancin kai ita ce saka ɗanmbar fito da su da yawa.