Asusun Tallafa Wa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce bai wa yara abinci mai gina jiki cikin kwanakin dubu 1000 na farko bayan haihuwarsu na taimakawa matuƙa wajen bunƙasar ƙwaƙwalwa da haɓakar giraman jikinsu.
Jami’ar kula da ingantaccen abinci kuma wakiliyar UNICEF a Kano, Abigail Nyam, ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin wani taron na kwana biyu da a aka yi a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda Asusun ya tattauna da shugabannin sashen labarai da na shirye-shirye na kafafen yaɗa labarai daga jihohin Kano da Katsina da Jigawa domin haɗa kai wajen wayar da kan al’umma da ma gwamnatoci game da muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar yara.
Jami’ar ta kuma bayyana illar da ke tattare da rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki ga yara, musamman daga lokacin da suke ciki da bayan haihuwa wanda kan shafi hazaƙar yara da ma girman jikinsu.
Ta ce hakan ne ke sa wasu yaran su zama ba su da ƙoƙari a makaranta ko kuma rashin girma idan aka kwatanta su da takwarorinsu da ke matakin shekaru ɗaya da suka samu abinci mai gina jiki.
Kuma wannan illa ba ta tsaya ga yarinta ba kaɗai, domin bincike ya tabbatar da cewa rashin samun ingantaccen abinci a cikin kwanaki 1000 daga haihuwa na shafar mutum bayan ya girma, inda mafi yawa ke fuskantar barazanar saurin kamuwa da cutattuka kamar na cutar suga da hawan jini da cutattuka da kan shafi zuciya da makamantance.
A cewar Nyam, hukumar lafiya ta duniya ta ba shawarci iyaye fara ba wa jariransu mama a cikin sa’ar da aka haife su da kuma shayarwa da keɓantaciya ta nonon mama zalla na watannin shidan farko bayan haihuwa tare da fara ba shi abinci haɗi da nonon mama har zuwa lokacin da zai cika shekaru biyu da haihuwa, domin kare lafiyarsa da kuma samun ingantacciyar lafiyar ƙwaƙwalwa da haɓakar jiki.
A yayin taron, shi ma jami’in hulɗa da Jama’a na UNICEF mai kula da jahohin Kano da Katsina da Jigawa, Mista Samuel Kaalu, ya gabatar da maƙala kan matsalar bahaya a sarari wanda ya koka yadda rahotanni suka tabbatar da cewa ɗaya ne cikin huɗu ne na mutane ke ƙaurace wa yin bahaya a sarari.
Sannan ya ce kowanne bahaya na ɗauke da miliyoyin kwayoyin cuta daban-daban kuma idan aka yi rashin Sa’a suka gurɓata ruwan da mutane ke sha, sai nan da nan a samu ɓarkwar cututtuka kamar ƙwalara.
Haka zalika, ya bayyana cewa alƙaluma sun nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 46 ne ke da ɗabi’ar yin bahaya a sarari kuma hakan ne ya sa tun a shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta ba da umarnin ɓullo da shiri na musamman wanda Ma’aikatar Ruwa ta Ƙasa ta ƙaddamar da wani shiri na tabbatar da tsabtar muhalli da aka kira da Clean Nigeria Campaing (CNC) wanda ciki har da batun magance bahaya a sarari a shekarar 2025.
Sai dai izuwa yanzu akwai sauran rina a kaba, domin shekaru 10 kenan ba tare da an kawo ƙarshen wannan matsalar ba.
Game da sha’anin ilimin yara kuwa, jami’in Asusun UNICEF mai kula da harkokin ilimi a Najeriya, Michael Banda, cikin maƙalar da ya gabatar ya nuna damuwarsa game da ƙaruwar yaran da ke gaza kammala karatu a matakin farko da kuma rashin ingancin karatu.
Ya ce kaso 70 cikin 100 (3 cikin yara 4) da ke tsakanin shakaru 7-14 ba sa iya karanta abu su fahimta da gaza yin lissafi mai sauƙi. Haka kuma kawo batun buƙatar ganin yara na kammala makarantunsu tare da samun ƙwarewa ta wani za su iya yi a matsayin sana’a.
Ita kuwa Fatima Musa Muhammad, ƙwararriya kan dokoki da tsare-tsaren ayyukan da kan shafi al’umma da ke Kano, ta bayyana muhimmancin sauƙewa da kiyaye haƙƙoƙin yara da suka rataya a kan iyaye da al’umma da irin rawar da gwamnati za ta taka wajen taimaka musu sauke wannan nauyi.
Ta ce haƙƙoƙin yaran sun haɗa da:
– ‘Yancin rayuwa: Yara na da haƙƙin a samar musu da abubuwan da za su tallafa wa rayuwarsu kamar abinci mai gina jiki da wurin kwana da lafiya da wadaccen tsari na rayuwa kamar yadda ya dace.
– Haƙƙin ciyar da su gaba: wannan ya shafi batu na ilimi da yin wasa da harkoki na al’adu, samun bayanai, ‘yancin bayyana tunaninsu da addini da sauransu.
Haƙƙin Samun Kariya: wajibi ne a tabbatar da kare yara daga kowanne na’i na cin zarafi da saryar da rayuwarsa da kula da yaran da ke sansanin ‘yan gudun hijira da tabbatar da adalci wajen hukuncin manyan laifuka da aikatau da kuma kowanne irin yunƙuri na ci-da-gumin yara.
Haƙƙin damar shiga a dama da su da bayyana ra’ayoyinsu da ba su damar bayyana ra’ayinsukan abin da ya shafi rayuwarsu da samar musu da damar shiga harkokin yau da kullum na al’umma.
Fatima ta kuma yi ƙarin haske kan gidauniyar tallafa wa yara ta baiɗaya, inda ta yaba wa gwamnatin jihar Kano shiga sahun farko na shan alwashin samar da hanyoyin da za su sauƙaƙa wa yara samun kiwon lafiya da kuma ilimi a matsayin wata hanya ta buƙasa rayuwar bil’adama.
“Wannan gidauniya za ta riƙa tallafawa iyaye ne da masu kula da yara ta hanyar ba su kuɗin a hannunsu domin tallafa wa yaran wajen samun ilimi da kiwon lafiya.
A ƙarshe, masu ruwa da tsaki na kafafen yaɗa labarai daga jihohin Kano da Katsina da Jigawa sun yi alƙawarin ganin sun tallafa wa Asusun Yara na UNICEF domin wayar da kan al’umma kan abubuwan guda biyar da aka tattauna a kan su a yayin wannan zama:
Abinci mai gina jiki
Matsalar yara da ke daina zuwa makaranta
Allurar riga-kafi (musamman foliyo)
Kawo ƙarshen matsalar bahaya a sarari.
Ginshiƙan matsaloli da ke tagayyara yara (lafiya, abinci mai gina jiki da Ilimi da ruwan sha da tsabtar muhalli da wurin kwana da samun bayanai da ba wa yara kariya).