Home » Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara gyaran tituna a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara gyaran tituna a Najeriya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara gyaran tituna a Najeriya

Ministan ayyuka na Najeriya, David Umahi, ya roƙi ‘yan Najeriya da su fara shirin bibiyar ayyuka na gina hanyoyi waɗanda za a fara yi a faɗin ƙasar nan.

A cikin jawabin da ministan ya yi, ya ce, nan ba da daɗewa ba za a fara aikin gyaran manyan hanyoyi mallakin gwamnatin tarayya a ƙasar nan bayan amince wa hukumarsa wajen kashe naira biliyan ɗari 300 a cikin ɗan ƙwarya-ƙwaryar ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2023 da aka yi.

Ya kuma ba da tabbacin karrama duk ɗan Najeriya da ya ba da sahihin rahoto game da ‘yan ƙwangilar da aka samu da yin aikin baban giwa, wato aiki marar inganci a faɗin ƙasar nan.

Ya ce za a  kashe naira biliyan ɗari ne wajen gyaran manyan titunan a jihohi 36 ciki har da babban birnin tarayya Abuja da suka lalace, inda za a kashe Naira biliyan ɗari 200 wajen cigaba da ayyukan da gwamnatin ta gada masu muhimmanci da ba a ƙarasa ba.

Kuma tuni shugaban ƙasa ya ba da umarnin cewa lallai ne a fara ayyukan kafin ɗaya ga watan Disambar shekarar nan da muke ciki ta bin hanyoyin da suka dace kuma a cewar ministan tuni aka fara ayyukan.

Sannan ya ce al’umma za su iya fara zagawa domin sanar da hukuma halin da waɗannan ayyuka suke ciki tare da roƙon al’umma kan su ɗauki hotunan duk wasu tituna da aka yi marasa inganci tare da aikewa zuwa ga waɗannan lambobi: 08030986263 ko 08037086137 ko kuma 08106423197 da kuma bayyana sunan kanfanin da ke aikin kwangilar, da wuri da abin da mutum ya lura da shi game da hanyar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?