Akalla mutane bakwai (7) ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu goma sha huɗu (14) suka jikkata, sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Yakasawa, da ke ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Hatsarin ya rutsa da wata motar Golf 3 Wagon da kuma motar bas kirar Toyota Sienna, inda rahotannin farko ke nuna cewa gudun wuce sa’a ko tsallake-tsallake ba bisa ƙa’ida ba na iya haddasa aukuwar hatsarin, duk da cewa hukumomi na ci gaba da bincike.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci mafi kusa domin samun kulawar likitoci, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiye gawa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana cewa rundunar ta fara bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Ya kuma nuna damuwa kan yawaitar haɗurra a kan hanyar Dutse–Ringim–Taura, inda ya ce wannan shi ne hatsari na uku cikin kwanaki bakwai (7) da suka gabata.
A cewarsa, mutane akalla 22 ne suka rasa rayukansu a jerin haɗurran da suka faru a Dutse, Ringim da Taura, waɗanda suka haɗa da motocin Golf da kuma motocin Tipper.
Rundunar ‘yan sanda ta yi kira ga direbobi da su bi dokokin tuki, su guji gudun wuce sa’a da tuƙi cikin sakaci, tare da tabbatar da cewa motocinsu na cikin koshin lafiya kafin fita hanya.
Haka kuma, mazauna yankin sun roƙi hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ɗaukar matakan kare haɗurra, domin hana ci gaba da salwantar da rayukan jama’a a kan wannan muhimmiyar hanya.
