• Home  
  • An karya dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela – MDD
- Babban Labari - Labarai

An karya dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela – MDD

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna damuwa cewa ba a mutunta dokokin ƙasa da ƙasa ba kan abin da Amurka ta aikata a Venezuela. António Guterres ya bayyana haka ne a wani sako da aka karanta a taron gaggawa da majalisar ta kira kan batun na Venezuela. “Abin damuwa ne matuka kan rashin mutunta […]

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna damuwa cewa ba a mutunta dokokin ƙasa da ƙasa ba kan abin da Amurka ta aikata a Venezuela.

António Guterres ya bayyana haka ne a wani sako da aka karanta a taron gaggawa da majalisar ta kira kan batun na Venezuela.

“Abin damuwa ne matuka kan rashin mutunta dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela.

“Lamarin zai iya janyo rashin daidaito a ƙasar, tasiri mara kyau a yankin da kuma yadda batun zai iya sauya yanayin dangantaka tsakanin ƙasashe,” in ji Guterres.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai