Daga majalisar wakilan Nijeriya kuma, ɗan takarar kujerar kakakin majalisar, wanda kuma shi ne ɗan takarar da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ke mara wa baya, Hon. Tajuddeen Abbas ya lashe zaben Shugaban Majalisar Wakilai ta 10 da kuri’u 353.
Hon. Abbas ya lashe zaben ne bayan doke abokan takararsa Ahmed Idris Wase da Aminu Sani Jaji a yau Talata.