Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta roƙi Hukumar Shige da Fice ta Najeriya da ta tabbatar da sauƙaƙen tsari da ingantaccen aiki yayin tantance maniyyatan Hajjin 2026 a filin jirgin sama.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta jihar a hedikwatar hukumar.
A yayin taron, sun tattauna kan dabarun ƙara inganta tsaro da kuma haɗin gwiwa domin tabbatar da an gudanar da Hajjin 2026 cikin nasara ba tare da tangarda ba.
Alhaji Labbo ya jaddada muhimmancin samar da na’urorin tantancewa na zamani da kuma tsare-tsare masu sauƙi domin rage jinkiri ga maniyyata, tare da tabbatar da suna kammala dukkan matakan bincike cikin lokaci kafin tashin jirgi zuwa ƙasar Saudiyya. Ya ce hakan zai rage wahala da cunkoso da ake fuskanta a lokutan tashi.
Haka kuma, ya buƙaci dukkan hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin maniyyata tun daga sansanin alhazai har zuwa filin jirgin sama kafin tafiya zuwa Saudiyya.
Ya gode wa hukumomin tsaro bisa irin goyon bayan da suke bai wa hukumar, tare da fatan Allah Ya ba da nasarar gudanar da Hajjin 2026 cikin kwanciyar hankali.
A nasu ɓangaren, hukumomin tsaron sun tabbatar da ba da cikakken goyon baya ga hukumar, inda suka yi alƙawarin tabbatar da tsaro da jin daɗin maniyyatan Jigawa a duk tsawon lokacin aikin Hajji.

