• Home  
  • Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya koma APC
- Babban Labari - Labarai

Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya koma APC

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC a hukumance. A jawabin da ya yi wa al’ummar jiha a ranar Juma’a, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito. Sauya shekar […]

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC a hukumance.

A jawabin da ya yi wa al’ummar jiha a ranar Juma’a, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin sauya sheƙar wasu gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria.

A baya-bayan nan ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki jihar, tare da ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan ya gabatar, matakin da wasu ke ganin tamkar zawarcin gwamnan ne.

Matakin gwamnan na zuwa ne kwana biyu bayan kakakin majalisar dokokin jihar, Bathiya Wesley, ya fice daga PDP tare da wasu mambobin majalisar 13.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai