Hukumar kidaya ta kasa reshen Jahar kano ta musanta batun sanya addini ko kabilanci acikin jerin tambayoyin da za tayiwa mutane a lokutan kidayar yan nijeriya da aka shirya yi a wata mayun nan mai zuwa .
Jami’ar yada labarai ta hukumar kidayar reshen Jahar kano Jamila Abdulkadir sulaiman ce bayyana haka yayin da take tattaunawa ta musamman da wakilin muhasa Yasir Adamu