Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika ta saukar da gudumarta a kan kungiyar kwallon kafa ta kasar Libya bisa cin zarafi da wulakancin da suka yiwa kasar Najeriya.
Libya dai ta yi watsi da kasar Najeriya da nuna halin ko inkula bayan sun sauka kasar ta Libya.Sakamakon hakan yasa Najeriya ta tattaro kayanta ta dawo ba tare da ta fafata wasa da kasar ta Libya ba.
A wasan farko da aka fafata a lokacin da Najeriya ta karbi bakuncin kasar ta Libya ta lashe Libya daci 1 – 0 wasan da aka fafata a jihar Akwa Ibom.
Sakamakon wannan laifi da Libya ta aikata hukumar ta CAF ta ci tarar kasar Libya har dalar Amurka miliyan 10. Haka zalika wasan da kasar Libya za ta kara da Najeriya an yanke hukuncin za ayi wasan a can kasar Angola wato ba a gidan kowa ba.
Sai dai hukumar ta jawa kasar Libya kunne a kan matukar kasar ta Libya ta sake kwatanta irin wannan laifin to za a dakatar da kasar daga dukkanin harkokin wasanni har tsawon shekaru biyu.
Idan za a iya tunawa kasashen dake Arewacin Afrika sun saba yin irin wannan kyarar ga sauran kasashen nahiyar Afrika biyo bayan abubuwan dake faruwa idan ana fafata gasar Confederation da gasar Zakarun nahiyar Afrika ga kungiyoyin kwallon kafa.