Kwamitin Abinci Da Bunƙasa Aikin Noma A Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa Najeriya ta yi asarar abinci da zai iya ciyar da aƙalla mutane miliyan takwas a faɗin ƙasar.
Kwamitin ya bayyana cewa an yi asarar kimanin tan dubu 55 da ɗari 629 na abinci sakamakon ambaliyar ruwa.
Hukumar abinci da bunƙasa aikin noma ta Majalisar ɗinkin Duniya ce ta fitar da rahoton. Bugu da ƙari hukumar ta ce asarar kayan abincin da Najeriya ta tafka ta isa a ciyar da mutum miliyan takwas da rabi har na tsawon watanni shida.
Salisu Muhammad, shine mataimakin shugaban hukumar abinci da bunƙasa aikin noma a Najeriya ya ce, ɗumamar yanayi da hauhawar farashi da matsalar tsaro da kuma durƙushewar tattalin arziƙi, na daga cikin matsalolin da suka addabbi ɓangaren noma a Najeriya.
Ƙididdigar na zuwa ne albarkacin bikin Ranar Abinci ta Duniya, wanda ya mayar da hankali wajen kira ga gwamnati ta haɗa hannu da masana wajen magance ƙalubalen ƙarancin abinci, musamman abinci mai gina jiki
Hukumar ta bayyana gamsuwa da matakan da gwamnati ke ɗauka wajen wadata ƙasa da abinci, amma ta yi gargaɗin cewa dole sai ta ƙara ƙaimi domin cim ma hakan.
shekarar nan dai Najeriya ta fuskanci matsaloli na ambaliyar ruwa a wasu yankunan ƙasar, musamman a yankin Maidugurin Jihar Borno, inda ambaliyar ta salwantar da rayuwaka da dukiyoyin al’umma.