Hukumar NOA da rundunar sojoji sun ƙudiri aniyar haɗa kan jama’a da kuma sanya kishin ƙasa.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta jaddada aniyar ta na ci gaba da yin hadin gwiwa da rundunar sojin Nijeriya don karfafa hadin kai da kishin ƙasa.

Shugaban hukumar NOA, Mallam Lenre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi baƙuncin babban hafsan soji da farar hula manjo janar Musa Awal, a hukumar dake babban birnin tarayya abuja.

Issa-onilu ya yabawa manjo janar Musa Awal, bisa jajircewarsa na yin hadin gwiwa da NOA, tun bayan naɗa shi ,a sabon miƙami , inda ya tabbatar da cewa hakan ya nuna kyakkyawar fahimta kan hulɗar soji da farar hula wajen haɗa kan  jama’a da kuma sanya kishin ƙasa.

Anasa ɓangaren manjo janar Musa Awal, ya ce ziyarar tana nufin ƙara haɗin gwiwa da hukumar NOA, inda ya bayyana taikaicinsa kan yadda labaran Ƙarya ke ci gaba da yaɗuwa a shafukan sada zumunta, inda ya tabbatar da kuƙinrin rundunar sojin na tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *