• Home  
  • Tinubu ya gaji, ya kamata ya yi ritaya – Peter Obi
- Babban Labari

Tinubu ya gaji, ya kamata ya yi ritaya – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya haƙura da neman sake tsayawa takara a 2027, yana mai cewa “shugaban ya gaji kuma ba shi da karfin da zai iya magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.” Obi ya ce Tinubu na […]

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya haƙura da neman sake tsayawa takara a 2027, yana mai cewa “shugaban ya gaji kuma ba shi da karfin da zai iya magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.”

Obi ya ce Tinubu na yanzu ba irin wanda ya yi mulkin jihar Legas ba ne a baya.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Obi ya ce Najeriya na tafiya ne a hanya mara kyau, yana mai zargin gwamnatin Tinubu da gaza magance talauci, yunwa da rashin tsaro.

Ya ce rahotannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya sun nuna cewa miliyoyin ‘yan Najeriya na fuskantar talauci da ƙarancin abinci, amma maimakon mayar da hankali kan waɗannan matsaloli, ‘yan siyasa na tattaunawa ne kan siyasa maimakon muhimman batutuwa.

Obi ya kuma ce “magance matsalar tsaro ba zai yiwu ba sai an rage talauci tare da zuba jari mai yawa a ilimi da samar da ayyukan yi.”

Duk da yabon da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Tinubu kan kokarin tsaro, Obi ya ce abin da gwamnati ke yi a yanzu bai isa ba.

Ya jaddada cewa burinsa ba wai zama shugaban kasa ba ne kawai, illa ganin Najeriya ta samu ci gaba da zaman lafiya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai