Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) na fuskantar matsin lamba kan ta sake duba zaben shekarar 2023 da aka kammala, inda ake iƙirarin an tafka magudi.
Wasu kungiyoyin farar hula a kasar sun bukaci hukumar da ta tabbatar da cewa an samu kura-kurai a zaben, kuma ya kamata hukumar ta sake duba zarge-zargen da ake yi na murkushe masu kada kuri’a da sayen kuri’u bisa tanadin dokar.
Kungiyoyin sun hada da TMG, TI da kuma CISLAC.
Ssugaban gamayyar kungiyoyi Auwal Rafsanjanin na CISLAC, yace Dole ne INEC ta sake duba duk wasu shaidun da suka nuna na magudin zabe da aka gabatar a gabanta.
Kungiyoyin CSO sun bayyana cewa rashin tsaro, danne masu kada kuri’a da siyan kuri’u ya nuna yadda aka gudanar da zaben gwamna da aka kammala.
Kungiyar TMG ta ce ta baza jami’an sa ido 768 a fadin kananan hukumomi 768 na kasar nan domin sanya ido a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Ya kara da cewa hakan ya hana masu kada kuri’a sayen kuri’u a wannan rana. TMG ta ce ta lura da irin shirin da INEC ta yi game da samar da kayayyaki zabe musanman BVAS, sai dai kungiyar ta ce game da tsaro a ranar zaben 2023, zaben yana daga cikin zabukan da aka fi tayar da hankali a tarihin Nijeriya