Home » Jakadiyyar Ingila a Najeriya Ta Koka Game da Ƙarancin Mata a Harkar Siyasa

Jakadiyyar Ingila a Najeriya Ta Koka Game da Ƙarancin Mata a Harkar Siyasa

by Anas Dansalma
0 comment

Jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing ta ce an ƙi bai wa mata a ƙasar damar da ta kamata wajen ganin sun bayar da gudummawa domin ci gaban ƙasar.

Catriona Laing ta bayyana haka ne lokacin wata tattaunawa ta musamman da BBC, inda ta kuma nuna damuwa kan raguwar yawan matan da aka zaɓa ko bai wa muƙaman siyasa a gwamnatin Najeriya.

Tace ta  lura da cewa yawan matan da suka samu nasarar cin zaɓe zuwa majalisar tarayya a zaɓen da aka kammala, ya ragu matuka idan aka kwatanta da zaɓen 2019.

Ta ce hakan ya mayar da Najeriya baya a ɓangaren siyasa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?