Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta janye sakamakon wata daliba mai suna, Mmesoma Ejikeme, wacce ta zana jarrabawar shiga jami’a saboda yi wa kanta aringizon maki.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, ya rabawa manema labarai a Abuja.
jami’a ta Nijeriya ta yi barazanar kai matashiya kotu bayan ta gano cewa ta shirga karya tare da yin ikirarin ta samun maki 362 a jarrabawar UTME ta 2023.
Inda jaridun kasar nan da kafafen sada zumunta suka yi ta yada
labarai kan dalibar da cewa ta zo ta daya a jarrabawar JAMB a fadin kasar nan.
Wannan ne ya sa har wasu suka soma yi mata kyauta da
yunkurin daukar nauyin ci gaba da karatunta har ta kai ta samu kyautar Naira miliyan 3 daga hannun
Innocent Chukwuma, shugaban kamfanin kera motoci na Innoson.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin hukumar ta JAMB Fabian
Benjamin ya fitar, ya ce sakamakon jarrabawar da ake yadawa na matashiyar ba
gaskiya ba ne.
Fabian ya ce sakamakon yaudarar da matashiyar ta yi, har gwamnatin Anambra ta shirya karrama ta.