• Home  
  • Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88
- Labarai

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wata mata mai shekara 30, Success Olafemi, bisa zargin ƙoƙarin jan hankalin wata yarinya ’yar shekara bakwai, yayin da jami’an tsaro suka gano katunan ATM 88 mallakin bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗi daban-daban a hannunta. An kama matar ne a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, a yankin […]

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wata mata mai shekara 30, Success Olafemi, bisa zargin ƙoƙarin jan hankalin wata yarinya ’yar shekara bakwai, yayin da jami’an tsaro suka gano katunan ATM 88 mallakin bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗi daban-daban a hannunta.

An kama matar ne a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, a yankin Kara Makasia, kusa da sansanin Redeemed Christian Church of God (RCCG) da ke Jihar Ogun.

Rahotanni sun ce wata mata mai suna Tope Makinde, mazauniyar ƙauyen Iwe-Lepe da ke kan hanyar Sagamu, ce ta sanar da ’yan sanda lamarin da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Makinde ta shaida wa ’yan sandan cewa Olafemi ta je Ewu-Lisa ta Simawa da misalin ƙarfe 9:00 na safe, inda ake zargin ta yi ƙoƙarin jan hankalin wata yarinya mai suna Jumat, wadda ba a bayyana cikakken sunanta ba.

A cewar rahoton, wadda ake zargin ta yi amfani da takardun kuɗin Naira 200 da kuma ƙananan  Milo wajen jan hankalin yarinyar, kafin daga bisani aka cafke ta.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wata mata mai shekara 30, Success Olafemi, bisa zargin ƙoƙarin jan hankalin wata yarinya ’yar shekara bakwai, yayin da jami’an tsaro suka gano katunan ATM 88 mallakin bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗi daban-daban a hannunta.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000