Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA), reshen rundunar dabarun yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Jihar Kano, ta ce ta kama mutane 1,860 da ake zargi da hannu a harkokin miyagun ƙwayoyi, ciki har da mata 92, tare da ƙwace kilogiram 5,409.814 na miyagun ƙwayoyi daban-daban tsakanin watan Janairu da Satumban 2026.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar wadda Kakakin hukumar Abubakar Sadiq maigatari ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce ta samu gagarumar nasara a ayyukan kama masu laifi, gurfanar da su a gaban kotu, wayar da kan jama’a da kuma kula da masu fama da matsalar shaye-shaye.
Miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace sun haɗa da tabar wiwi (Cannabis sativa), hodar ibilis (Cocaine), methamphetamine da sauran ƙwayoyin da ke shafar tunanin ɗan Adam, da waɗanda doka ta haramta amfani da su.
Sanarwar ta ce a cikin watanni tara, hukumar ta samu nasarar hukunta mutane 89, yayin da ta shigar da sabbin shari’o’i 126 a gaban kotu. Haka kuma, akwai shari’o’i 135 da har yanzu suke gaban Babbar Kotun Tarayya.
Hukumar ta bayyana cewa alkaluman na nuna irin ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da bin dokokin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi bisa ƙa’idojin shari’a.
An gudanar da ayyukan wayar da kai 420
Baya ga kama waɗanda ake zargi, sashen ba da shawarwari, jinya da gyaran halayen masu fama da shaye-shaye na hukumar ya gudanar da ayyukan taimako kusan 1,700 domin tallafa wa mutanen da matsalar shaye-shaye ta shafa.
Haka kuma, hukumar ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kusan 420 a makarantu da cikin al’ummomi, domin ilmantar da matasa da sauran jama’a game da illolin shaye-shaye da muhimmancin ɗaukar matakan kariya.
An rushe maboyar masu sayar da miyagun ƙwayoyi 35
A wani ɓangare na ayyukanta, rundunar ta ce ta gudanar da samame na musamman domin rusa wuraren da ake sayarwa da rarraba miyagun ƙwayoyi a faɗin Jihar Kano.
Sanarwar ta ce a ƙarƙashin umarnin Shugaban Hukumar NDLEA na Ƙasa, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), CON, OFR, aikin Operation Restore Order ya taimaka wajen rusa kusan maboyar masu safarar miyagun ƙwayoyi guda 35 da aka gano, tare da kama mutum sama da 300 da ake zargi.
Hukumar ta ce aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na tarwatsa hanyoyin sadarwar masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma inganta tsaron al’umma.
An gano ramuka da koguna a Rimin Kebe
Haka kuma, a wani samame mai suna Operation Sharar Mafaka, hukumar ta ce ta gano ramuka da koguna a ƙarƙashin ƙasa a yankin Rimin Kebe, waɗanda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da su wajen gudanar da haramtattun ayyukansu a ɓoye.
A cewar hukumar, gano waɗannan wurare ya bayyana irin dabarun da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da su wajen ɓoye ayyukansu, tare da nuna ƙalubalen da ake fuskanta wajen tarwatsa gungun masu aikata irin waɗannan laifuka.
NDLEA ta jaddada cewa dabarun yaƙi da miyagun ƙwayoyi ba su tsaya ga kama masu laifi da gurfanar da su a gaban kotu kaɗai ba, domin sun haɗa da wayar da kan jama’a, ba da shawarwari, jinya da gyaran halayen waɗanda suka kamu da shaye-shaye.
Kwamanda ya yaba wa Gwamna Abba da sauran masu ruwa da tsaki
Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, CN DY Lawal, ya nuna godiyarsa ga Shugaban Hukumar na Ƙasa, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), bisa jagoranci da jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan hukumar.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sauran masu ruwa da tsaki, al’ummomi da kafafen yaɗa labarai bisa haɗin kai da gudummawar da suke bayarwa wajen yaƙi da shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi.
Kwamandan ya yi kira ga mazauna Kano da su ci gaba da bai wa hukumar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka mata wajen gano masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma yaƙi da shaye-shaye.
