Home » Kaduna: Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Fashin Daji

Kaduna: Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Fashin Daji

by Anas Dansalma
0 comment

Rundunar sojin Najeriya da ke jihar Kaduna ta ce ta kashe ‘yan fashin daji biyar tare da ƙwato makamai a wani samame da ta kai dajin Kubusu da kuma tsaunukan Kaso a yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar.

A wata sanarwa da mai riƙon muƙamin jami’in hulda da jama’a na runduna ta 1 da ke Kaduna Laftanar Kanal Musa Yahaya ya fitar, ya ce dakarun sojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 shida, da harsasan bindigogin shida, da wasu ƙarin harsasan, da babura uku wasu kayyakin.

“A lokacin ba-ta-kashi da ‘yan fashin wanda ya ɗauki sa’o’i, dakarun sojin sun samu nasarar fatattakar ‘yan fashin, tare da kashe biyar daga cikinsu, sannan suka ƙwato makamai masu tarin yawa a lokacin fafatawar”, kamar yadda sanarawar ta bayyana.

Daga ƙarshe sanarawar ta ambato babban kwamandan runduna ta 1 da ke Kaduna Manjo Janar Taoreed Lagbaja na yaba wa dakarun sojin bisa wannan namijin ƙoƙari da ya ce sun yi a lokacin fafatawar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi