Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar nan ta kori ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar don ƙalubalantar Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya.
Abdussalam Abdulkarim da aka fi sani da AA Zaura na jam’iyyar APC ne, ya shigar da ƙarar saboda dalilai da dama ciki har da cewa ba a tura sunan Sanata Rufa’i Sani Hanga zuwa hukumar zaɓe a kan lokaci ba, don haka ya nemi kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.