Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan jihar ta gabatar da rahoton ta ga ma’aikatar shari’a kan zargin kisan da ake yi wa, Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ƙarbi takardar bayanan a ofishinsa ranar Juma’a 19 ga watan Mayun 2023, Antoni Janar ɗin ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sanda jihar ya kawo takardar bayanan.
Ya ce kwamishinan ya kawo takardar da ke ɗauke da bayanan ne da misalin ƙarfe 12:45 na ranar Juma’a.
Kwamishinan Shari’ar jihar ya sanar da cewa ma’aikatar ta sake mayar da rahoton ga ƴan sanda domin su ci gaba da bincike, inda ta nemi samun ƙarin bayani kan zarge-zargen da ake yi wa Doguwa waɗanda za su bayar da hurumin gurfanar da shi a gaban kotu.
Daga cikin bayanan da ma’aikatar shari’ar ta buƙata har da hotunan gawarwakin waɗanda aka kashe, bayanan shaidu da bindigar da aka kwato da sauran abubuwan da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifukan, domin tabbatar da an aikata laifin kamar yadda ake tuhuma