Home » Koken Yan Nijeriya Ya Sanya EFCC Binciken Kamfanin CBEX

Koken Yan Nijeriya Ya Sanya EFCC Binciken Kamfanin CBEX

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta sanar da fara gudanar da bincike kan yadda wasu ƴan Najeriya ke ci gaba da ƙorafe-ƙorafe kan asarar da suka tafka a dandalin saka hannun jari na CryptoBank Exchange (CBEX), hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta sanar da fara gudanar da bincike kan lamarin.

Rahotanni sun ce kuɗin da ‘yan Najeriya suka yi asara a dandalin na CBEX sun kai sama da naira tiriliyan ɗaya.

Hukumar ta shaida wa BBC cewa ta haɗa hannu da rundunar ƴansanda ta ƙasa da ƙasa INTERPOL da hukumar FBI ta Amurka domin yunƙurin gano waɗanda ke da hannu a dandalin na CBEX tare da ganin yiwuwar karɓo wasu kuɗaɗen da suka maƙale.

Hakan na zuwa ne bayan ƙorafin da waɗanda suka sanya hannun jari a dandalin suka yi na cewar sun kasa cire kuɗaɗen da suka sanya.

Mutane da dama sun tafka mummunar asara bayan sun zuba maƙudan kuɗi a dandalin, sakamakon alƙawarin da aka yi musu cewa za su samu ribar kashi 100 bisa 100 na kuɗaɗen da suka sanya cikin wata guda

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?