• Home  
  • Kotu Ta Daure Direban Jirgin Kasa Watanni 18 A Legas Saboda Satar Kuɗi
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Daure Direban Jirgin Kasa Watanni 18 A Legas Saboda Satar Kuɗi

Wata kotu a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ɗaure wami direban jirgin ƙasa wata 18 a gidan yari saboda kama shi da laifin satar kuɗi. Mai Shari’a Rahman Osodi na kotun da ke Ikeja ta kama Christopher Ekene Ofielu mai shekara 39 da laifin satar naira miliyan 6.9 a ranar Litinin da ta […]

Wata kotu a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ɗaure wami direban jirgin ƙasa wata 18 a gidan yari saboda kama shi da laifin satar kuɗi.

Mai Shari’a Rahman Osodi na kotun da ke Ikeja ta kama Christopher Ekene Ofielu mai shekara 39 da laifin satar naira miliyan 6.9 a ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci ta ruwaito a yau Asabar.

Ɗaya daga cikin laifuka uku da kotun ta kama shi da su na tuhumar sa da tura kuɗin zuwa asusun ajiyarsa na banki daga dandalin HabariPay Ltd ba bisa ƙa’ida ba.

Lauyansa ya nemi alƙalin ya sassauta masa kasancewar ya yi nadama kuma shi ne karon farko da aka gurfanar da shi a gaban kotu.

Wannan ta sa mai shari’ar ya yanke masa hukuncin wata 18 a gidan yari, ko kuma biyan tarar naira miliyan ɗaya da rabi bisa sharaɗin sai ya mayar da kuɗin da ya sata cikin mako ɗaya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000