• Home  
  • Kotu ta hana a yi belin Abubakar Malami
- Babban Labari - Labarai

Kotu ta hana a yi belin Abubakar Malami

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar neman beli da tsohon ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami ya yi domin sakin sa daga hannun hukumar EFCC. Mai Shari’a Babangida Hassan ya ce bai zai iya amince wa da buƙatar belin ba saboda doka ta bai wa hukumar EFCC ta tsare tsohon ministan […]

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar neman beli da tsohon ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami ya yi domin sakin sa daga hannun hukumar EFCC.

Mai Shari’a Babangida Hassan ya ce bai zai iya amince wa da buƙatar belin ba saboda doka ta bai wa hukumar EFCC ta tsare tsohon ministan shari’ar domin ci gaba da bincike.

Tun dai ranar 8 ga watan Disamba Abubakar Malami ke tsare a wurin hukumar ta EFCC.

A ranar Laraba ne Malami ya kwarmata cewa jami’an hukumar sun kai samame ofishinsa da gidajensa da ke Abuja da Kebbi.

EFCC na riƙe da malami ne kan tuhumar laifuka guda uku waɗanda tsohon ministan ya musanta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai