• Home  
  • Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe
- Babban Labari - Siyasa

Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe

Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta rushe takarar Farfesa Isa Ali Pantami ɗantakarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna […]

Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta rushe takarar Farfesa Isa Ali Pantami ɗantakarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Gombe.

Wani makusancin Farfesa Pantami da BBC ta zanta da shi ya ce tawagar lauyoyin ɗantakarar na PDP na nazarin hukuncin.

Kotun ta buƙaci jam’iyyar PDP ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani domin tabbatar da wanda zai yi wa jam’iyyar takara

A watan Yuni ne PDP ta bai wa Pantami tikitin takarar gwamnan Gombe bayan da ya gaza samu tikikin jam’iyyar APC.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai