Wata kotu a jihar Osun ta yanke wa wani malamin tsibbu mai suna Kabiru Ibrahim hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samun shi da laifin kashe wani abokin hulɗarsa mai suna Lukman Adeleke.
Kotun mai zaman a garin Iwo dai ta yanke masa hukuncin ne bayan samun shi da laifukan hada baki, da kisan kai da kuma sata.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Justice Lateef Adegoke ya ce masu shigar da ƙara sun tabbatar da hujjojin da ke nuna cewa malamin ya aikata kisa da kuma sata.
Saboda haka Justice Adegoke ya yanke ma sa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai kan sata da kuma kisa ta hanyar rataya saboda kisan kisan kai.
Wata sanarwa daga ma’aikatar sharia ta jihar Osun ta ce lauyoyin gwamnati sun shaida wa kotun cewa Kabiru Ibrahim, malamin marigayi Adeleke ne kuma ya fada masa shirin da yake na sayen wani fili ne, sai malamin ya ce masa ya zo da kudin da dare a yi musu addu’a kafin ya je ya biya filin.
Iyalin wanda aka kashen sun ce Adeleke ya yi ɓatan dabo bayan tafiya wurin malamin don yi ma sa addu’a abin da ya sa suka kai ƙara wajen ‘yansanda.
Sanarwar ta ce a yayin tambayoyin da ‘yansanda suka yi wa malamin tsibbun ne ya yi ikrarin cewa ya kashe mutumin.
Daga nan kuma ya kai jami’ai wani wuri inda aka ga gawar Adeleke cikin wani buhu a gefen babbar hanyar Ilesa zuwa Akure.

