Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Ikot Ekpene na jihar Akwa Ibom sun yi watsi da shirin baiwa ɗan takara tikitin kai tsaye domin kujerar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Ikot Ekpene/Obot Akara, gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, inda suka bayyana hakan a matsayin saɓawa ka’idojin dimokuraɗiyya.
An bayyana matsayar ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Talata, domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar a yankin.
Masu ruwa da tsakin sun mayar da martani ne ga rahotannin da ke cewa gwamnan jihar, Umo Eno, ya umarci shugabannin jam’iyyar a wurare daban-daban da su rungumi tsarin tsayar da ɗan takara ta hanyar yarjejeniya domin wakiltar jam’iyyar a zaɓen fidda gwani.
Sai dai tsohon mataimakin sakataren APC kuma kakakin ƙungiyar, Ubong Amadu, wanda ya karanta sanarwar a wani taron manema labarai da aka gudanar a otal ɗin Four Points by Sheraton da ke Ikot Ekpene a ranar Alhamis, ya jaddada cewa tsarin yarjejeniya na tauye muradin mafi rinjayen ‘ya’yan jam’iyya.
Amadu ya kuma bayyana cewa tsarin zaɓen fidda gwani kai tsaye yana da fa’ida, yana mai cewa tsarin yarjejeniya ya saɓa da ka’idojin adalci da aka tanada a kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokar zaɓe ta shekarar 2026.
Sanarwar, wadda shugabannin masu ruwa da tsaki na APC a Ikot Ekpene suka sanya wa hannu, ta ce a wani ɓangare “Bayan lura da rahotannin da ke nuna cewa wasu na ƙoƙarin ƙaƙaba wani ɗan takara ta hanyar tsarin yarjejeniya wanda ba shi da farin jini kuma ba na dimokuraɗiyya ba, ya sa ya zama dole a gudanar da wannan taro.”
Hakazalika, masu ruwa da tsakin sun bayyana goyon bayansu ga takarar wa’adi na biyu na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da kuma Gwamna Umo Eno, bisa la’akari da ayyukan da suka gudanar a ofisoshinsu.
