• Home  
  • Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.
- Babban Labari

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 490 da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan NEXIM Bank, Robert Orya, kan almundahanar Naira biliyan 2.4. Kotun ta yi watsi da ƙarar da Orya ya shigar, tare da tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya na ranar 5 ga Fabrairu, 2026. […]

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 490 da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan NEXIM Bank, Robert Orya, kan almundahanar Naira biliyan 2.4.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da Orya ya shigar, tare da tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya na ranar 5 ga Fabrairu, 2026.

An samu Orya da laifi kan tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da yaudara, ƙirƙirar takardun bogi da damfarar kuɗi. An yanke masa shekaru 10 a kan kowanne tuhume-tuhume, amma hukuncin zai gudana a lokaci guda, don haka ba zai yi shekaru 490 a gidan yari ba.

Orya ya kasance Manajan Daraktan NEXIM Bank daga 2009 zuwa 2016.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai