Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 35, Adamu Musa, bisa zargin yin karyar cewar shi, babban jami’in ’yan sanda da kuma damfarar jama’a da sunan samar musu da aikin ’yan sanda da sauya wurin aiki.
An kama Adamu, mazaunin Kureken Sani Quarters a Kano, a ranar 1 ga Satumba 2026, bayan rundunar ta samu bayanan sirri cewa yana yawo yana gabatar da kansa a matsayin Chief Superintendent of Police (CSP).
Kakakin rundunar yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce jami’an sashen yan sandan Panshekara ne suka kama wanda ake zargin, bayan samun rahoton daga rundunar yan sandan kwantar da tarzoma ta 52, Mobile Force da ke Challawa.
Binciken farko ya nuna cewa Adamu na amfani da hotunan bogi da aka gyara da fasahar AI, inda yake haɗa hotonsa da na manyan jami’an ’yan sanda, domin ya shawo kan mutane cewa yana da iko da damar taimaka musu wajen samun aikin ’yan sanda ko sauya musu wurin aiki.
A yayin bincike a gidansa, ’yan sandan sun kwato riga da wando na yan sanda, takalma baƙake guda biyu da kuma Naira 300,000.
Rundunar ta ce wanda ake zargin yana tsare, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su yi hattara da masu amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar hotunan bogi, musamman wajen neman kuɗi da sunan ɗaukar aiki ko sauya wurin aiki a Rundunar yan yandan Najeriya.
Rundunar ta jaddada cewa ɗaukar aiki a ’yan sanda kyauta ne, don haka babu jami’in da ya dace ya nemi kuɗi daga mai neman aikin ’yan sanda.
